Lokacin Da Mai Taimakonta Ya Bace

Birbishin Rikici by HumAngle

Episode notes

Ka gudu don ceton rayuwarka lokacin da Boko Haram suka kai hari a garinku a Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya. Da ka dawo, sai ka tarar da makwabci ya fara gina gida a kan filin ka.

Lokacin da ka nuna rashin amincewa, ya ba wa jami’ai cin hanci kuma ya kore ka, yana cewa ba ka da wani da zai gaji gidan. Ɗanka, wanda shi ne babban mai kula da kai, ya ɓace a lokacin yaƙin, kuma har yanzu ba ka ji labarinsa ba.

Wanne ciwo ne yafi nauyi: jimamin rasa wanda kake kauna da ba ka san ko yana raye ba ko kuma wahalhalun rayuwar yau da kullum da suka biyo bayan rasa mai kula da kai? Duk hanyoyin, sakamakon suna da matuƙar nauyi. To, ta yaya za ka jure wa baƙin ciki, talauci, da rashin adalci duka a lokaci guda?