Birbishin Rikici

Birbishin Rikici

by HumAngle
Season 1
Ta Rasa Komai Dalilin Boko Haram
Gina Bashir manomiya ce mai shekaru 46 daga Askira Uba a jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya. A lokacin da rikicin Boko Haram ya kai kololuwa, tana zaune a Benisheik, wani karamin gari a Borno, tare da mijinta da ‘ya’yanta shida. A lokacin wannan rikici, ta rasa dan’uwanta, dan dan’uwanta, da wasu ‘yan uwa shida. A cikin wannan bidiyo, mun tattauna game da yadda ta tsira da kuma burinta ga ‘ya’yanta.
Gudun Tsira
Kina dauke da ciki na watanni tara, ba takalmi a ƙafa, kina gudu cikin ƙaya, kura da tsoro. Kusan shekaru goma, Ya Busam Ali ta shafe tana rayuwa a matsayin yar gudun hijira, tana tafiya me nisa a kowace kakar noma zuwa gonakin da ‘yan ta’adda ke iko da su, domin kawai ta kula da kanta da ‘ya’yanta. Wannan shirin na #BirbishinRikici ya bi labarin yadda ta tsira, juriyarta, da ƙarfin zuciyar da ke tura ta ci gaba da tafiya duk da ƙalubalen da ke gabanta.
Lokacin Da Mai Taimakonta Ya Bace
Ka gudu don ceton rayuwarka lokacin da Boko Haram suka kai hari a garinku a Adamawa, arewa maso gabashin Najeriya. Da ka dawo, sai ka tarar da makwabci ya fara gina gida a kan filin ka. Lokacin da ka nuna rashin amincewa, ya ba wa jami’ai cin hanci kuma ya kore ka, yana cewa ba ka da wani da zai gaji gidan. Ɗanka, wanda shi ne babban mai kula da kai, ya ɓace a lokacin yaƙin, kuma har yanzu ba ka ji labarinsa ba. Wanne ciwo ne yafi nauyi: jimamin rasa wanda kake kauna da ba ka san ko yana raye ba ko kuma wahalhalun rayuwar yau da kullum da suka biyo bayan rasa mai kula da kai? Duk hanyoyin, sakamakon suna da matuƙar nauyi. To, ta yaya za ka jure wa baƙin ciki, talauci, da rashin adalci duka a lokaci guda?
Neman Yanci Da Kudin Fansa
kuna gida kuna shirye-shiryen dare, bayan sallar isha'i. Rayuwarku na cike da kalu-bale, amma aƙalla kuna tare da iyalan ku. kwatsam, ba tare da gargadi ba, mahara dauke da makamai suka mamaye kauyen ku. Suna baku umarni da ihu har baku iya gane me suke fada. Tsoro ya ratsa jikinku. Kuna gudu cikin duhu, zuciyar ku tana bugawa tare da fatan tsira, kuna ta addu'a. Amma duhun dare be baku abin da kuke fata ba. Yan ta’addan sun gan ku, kuma Suka fito da ku! Daga wannan lokacin, rayuwa kamar yadda kuka sani ta canza muku gaba ɗaya. Wannan Jigon na #BirbishinRikici ya bada labarin Huaraira da kwanakin da tayi a tsare.
Kwana Na Karshe A Gida
kina gida tare da mijinki da 'ya'yanku hudu, kuna shirya abincin rana kamar kowace rana. Kwatsam sai kuka ji 'yan ta'adda dauke da makamai sun kewaye garinku. Suna afkawa gidaje, suna sace amfanin gona, suna kashe duk wanda ya musu gadara. Take kuka fita da gudu zuwa cikin daji. Jama'a duk an watse zuwa wurare daban-daban. A wannan yanayi kika nemi mijinki kika rasa, sai bayan lokacin da abun ya lafa, sai aka ce an gano gawar mijinki. Wajen da kike kira gida yanzu ba tsaro, don haka kuka yi hijira don sake gina rayuwa daga farko. Amma me farawa daga farko ke nufi?
Masu Kewa Da Wadanda Suke Kewarsu
Explicit
Lokacin da wanda kuke ƙauna ya ɓace, kuma bayan shekaru ba ku gan shi ko ji daga gare shi ba, baku cire ran sake haɗuwa, se ya zama wani jinkirin me zafain jira. Amma me zai faru idan an shafe fiye da shekaru goma ana jira bayan tuna su shine kadai alama ta cewa sun taba rayuwa?
Danta Ya Taka Bom!
Explicit
Kin yi aure da wani soja wanda kuka gina rayuwa da shi kuma kuka haifi ’ya’ya shida. wata rana, an tura shi yaki ba sake dawowa ba. Shekaru da yawa bayan haka, yayin da barazanar tayar da kayar baya ta fara bayyana a cikin garinku, ɗanku ya taka bam da ya fashe. Ba ku da tabbas ko zai tsira, kuka garzaya da shi asibiti a babban birnin tarayyar Najeriya, da fatan ba shi damar yin rayuwa. Bayan shekaru goma, har yanzu ba za ku iya komawa gida ba. Rikicin ya ci gaba da yaduwa. Yanzu, ana fitar da ku daga sansanin da kuke zama inda kuka zauna tsawon shekaru. Me zaku yi? Ina za ku je?
Gwagwarmayar Rayuwa
Explicit
Ke uwa ce mai yara takwas, kina rainon ‘ya’yanki a sansanin ‘yan gudun hijira dake babban birnin tarayyar Najeriya bayan tserewa mummunan harin da kungiyar ta’addancin Boko Haram ke kaiwa. Ta yaya zaki iya tinkarar barazanar rugujewar sansaninku, da kama danki, da kuma kwace baburan acabar da ki ka siya don samun abin rike rayuwa bayan duk kokarin ki na ganin kun samu rayuwa mai kyau na neman ya ci tura?
Labarin Jajircewa
Explicit
Me za ku yi a lokacin da ’yan Boko Haram suka sace danku suka kuma koya mishi musu yaki, alhali kuna fuskantar kora a gidanku? Wannan jigon na #BIRBISHINRIKICI ta bibiyi rayuwar Ya Hauwa, wacce ta zama mace tilo da ke aiki a matsayin wakiliya a Borno, arewa maso gabashin Najeriya.
Gudun Tsira Dauke Da Juna Biyu
Explicit
Jummai mai dauke da cikin wata tara ta tsere daga garinsu da ke Nassarawa a Arewacin Najeriya bayan jin karar harbe-harbe! Wannan ba shine karo na farko da take tserewa tashin hankali ba. A cikin wannan shirin na #BIRBISHINRIKICI, mun ba da labarin asarar da sukayi da kuma gudun hijira.
1 of 13