Esplicito
Ya Kubucewa Masu Garkuwa Ba Tare Da Biyan Fansa Ba
Note sull'episodio
A Arewa maso Yammacin Najeriya, yin garkuwa da mutane yana iya faruwa a ko'ina, ba wai zama a wurin da bai dace ba ne a lokacin da bai dace ba. Wani manomin shinkafa da masara mai suna Mustapha Shafi’i a garin ‘Yarkofoji na jihar Zamfara, yana cikin gidansa ne ‘yan ta’adda suka fasa masa kofarsa, suka kutsa kai, suka tafi da shi a lokacin da matarsa ke kallonsu tana rokon su sakeshi. Yayi sa'a, ya gudu har ya bada labarinsa.
Mai gabatarwa: Zubaida Baba Ibrahim
Marubuci: Kunle Adebajo
Muryoyin shiri: Aliyu Dahiru, Khadija Gidado, Isaac Oritogun
Fassara: Ruqayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: Ahmad Salkida