Hatsarin Noma A Inda Babu Tsaro

Birbishin Rikici by HumAngle

Episode notes

Da can kana shafe tsawon kwanaki a gona, kana shuka iri-iri na amfanin gona kana dawowa gida da girbi mai yawa. Yanzu kuma, sa’o’i kaɗan kacal kake aiki, a ƙarƙashin sa ido na sojoji. Ba za ka iya yin nesa da gari ba, kuma ba za ka ƙara shuka amfanin gona masu tsawo ba domin suna iya ɓoye ’yan ta’adda.

Saboda haka kana shuka wake da gyada kawai, amma amfanin da kake samu ba ya taɓa isa. Kuma duk lokacin da ka taka gona, ka san akwai yiwuwar ka ji karar harbe-harbe, sai ka tsere don ceton ranka.

A wannan shirin na #BirbishinRikici, mun ba da labarin Hannatu Isiah, wata manomiya a Madagali, wata ƙaramar al’umma a Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, wadda ta kasa ciyar da kanta ko samun kuɗin amfani sakamakon rashin tsaro.