Birbishin RikiciExplícito

por HumAngle

Kokarin nutsawa cikin wahalhalun da mutanen da ke zaune a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula ke fuskanta, yawanci yakan zo ne kawai ta fuskar kididdiga; Birbishin Rikici wani shiri ne na mako-mako akan waɗannan labarun sirri na wadanda rikici da tashin hankali suka shafa da HumAngle ke kawo muku.

Episodios del podcast

  • Temporada 1

  • Rayuwar Shekara Takwas Da Yaya Hudu A Hannun Boko Haram

    Explícito

    Rayuwar Shekara Takwas Da Yaya Hudu A Hannun Boko Haram

    Explícito

    A cikin shirin #BirbishinRikici, za mu kawo muku labarin Aisha, wacce aka yi garkuwa da ita tana da shekaru sha takwas, aka yi mata auren dole da wani dan Boko Haram. Bayan shekaru takwas, ta tsere a matsayin mahaifiyar 'ya'ya hudu. Yanzu, tana bin burinta da kwato 'yancinta. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: HumAngle Media

  • Bayan Kubutar Amaryar Da Yan Garkuwa Suka Yi Wa Fyade

    Explícito

    Bayan Kubutar Amaryar Da Yan Garkuwa Suka Yi Wa Fyade

    Explícito

    A shirin #BirbishinRikici na yau, muna ba da labarin Hauwa Abbagana, wata budurwar amarya da aka sace. Bayan tserewa daga zaman talala, ta dawo gida ciki da ɗan wanda ya zalunce ta, cikin fargabar kyama da ƙi da za ta iya fuskanta. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija Gidado, Samir Sheriff Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: HumAngle Media

  • Kisan Kiyashi A Ranar Kirsamati

    Explícito

    Kisan Kiyashi A Ranar Kirsamati

    Explícito

    Babu wanda ya ga hakan yana zuwa, yayin da mutanen kauyen suka shirya kansu domin murnar bukukuwan, ‘yan bindiga na kan hanyarsu ta zuwa yanka su. An kai wa kananan hukumomi uku hari a jihar Filato a Najeriya, inda aka kashe mutane kusan 195 da kuma abubuwan tunawa da mutane suka yi a kusa da gidajensu. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija Gidado, Hajara Ibrahim, Akila Jibrin Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: HumAngle Media

  • An Kone Musu Gida, An Kone Duk Burikansu

    Explícito

    An Kone Musu Gida, An Kone Duk Burikansu

    Explícito

    A shiri na yau, zamu ba da labarin Rukayya Saidu, wata uwa mai yara biyu da aka kona gidanta a Kaku, amma tana sake gina rayuwarta yanzu a Kajuru, Arewa maso Yammacin Najeriya. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Khadija Gidado Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: HumAngle Media

  • Yadda Ake Yi Wa Yan Kabilu Kudin Goro A Arewa Maso Yammacin Najeriya

    Explícito

    Yadda Ake Yi Wa Yan Kabilu Kudin Goro A Arewa Maso Yammacin Najeriya

    Explícito

    A yau za mu ji labarin Umar, wani Bafulatani da ya sha fama da hare-haren ta’addanci a kauyensu, sannan ya ga al’ummar da yake zaune a cikinsa sun juya masa baya ba gaira ba dalili sai asalinsa. Umar, kamar sauran jama’a, ya kasance wanda aka zalunta dan kabilanci. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Muryoyin Shiri: Akila JibrinFassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Khadija Gidado Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: HumAngle Media