Explicit
Rayuwa Tare Da Warin Gawa
Episode notes
A lokacin da ake fama da hare-haren Boko Haram a Najeriya, an samu asarar rayuka da dama. Binciken HumAngle ya gano cewa ana jibge gawarwaki da dama da ba a san ko su waye ba a asibitin kwararru na jihar Borno. Kusa da asibitin al’ummar Hausari ne, kuma suna da koke-kokensu.
Muryoyin Shiri: Akila Jibrin, Samir Sherrif, Aliyu Dahiru
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Khadija Gidado
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: HumAngle Media