Gudun Tsira Daga Yan Garkuwa
Birbishin Rikici di HumAngle
Note sull'episodio
A jigo na baya na #BirbishinRikici mun ba da labarin Bintu Suleiman, wacce aka yi garkuwa da ‘ya’yanta mata da jikokinta a lokacin harin da aka kai Ngoshe, a arewa maso gabashin Najeriya, a ranar 3 ga Maris, 2026. Har yanzu tana jiran labari, tana kuma fatan za su dawo.
Yanzu, mun dawo sabon bayani.
A cikin wannan shirin, ‘yarta mai shekaru 16, Aisha Muhammad Shuaibu, ta tsere daga hannun masu garkuwa da mutane bayan ta shafe tsawon watanni biyu da makonni biyu a hannun ‘yan ta’addan. Ta dawo gida ɗauke da ɗan’uwanta mai shekaru huɗu a bayanta.
Ta ba HumAngle labarin abin da ya faru da ita a lokacin da take tsare da masu garkuwa da su da kuma yadda ta samu damar tserewa.