
Birbishin Rikici
Explícito
por HumAngleKwana Na Karshe A Gida
kina gida tare da mijinki da 'ya'yanku hudu, kuna shirya abincin rana kamar kowace rana. Kwatsam sai kuka ji 'yan ta'adda dauke da makamai sun kewaye garinku. Suna afkawa gidaje, suna sace amfanin gona, suna kashe duk wanda ya musu gadara. Take kuka fita da gudu zuwa cikin daji. Jama'a duk an watse zuwa wurare daban-daban. A wannan yanayi kika nemi mijinki kika rasa, sai bayan lokacin da abun ya lafa, sai aka ce an gano gawar mijinki. Wajen da kike kira gida yanzu ba tsaro, don haka kuka yi hijira don sake gina rayuwa daga farko. Amma me farawa daga farko ke nufi?kina gida tare da mijinki da 'ya'yanku hudu, kuna shirya abincin rana kamar kowace rana. Kwatsam sai kuka ji 'yan ta'adda dauke da makamai sun kewaye garinku. Suna afkawa gidaje, suna sace amfanin gona, suna kashe duk wanda ya musu gadara. Take kuka fita da gudu zuwa cikin daji. Jama'a duk an watse zuwa wurare daban-daban. A wannan yanayi kika nemi mijinki kika rasa, sai bayan lokacin da abun ya lafa, sai aka ce an gano gawar mijinki. Wajen da kike kira gida yanzu ba tsaro, don haka kuka yi hijira don sake gina rayuwa daga farko. Amma me farawa daga farko ke nufi? Temporada 1
Masu Kewa Da Wadanda Suke Kewarsu
Lokacin da wanda kuke ƙauna ya ɓace, kuma bayan shekaru ba ku gan shi ko ji daga gare shi ba, baku cire ran sake haɗuwa, se ya zama wani jinkirin me zafain jira. Amma me zai faru idan an shafe fiye da shekaru goma ana jira bayan tuna su shine kadai alama ta cewa sun taba rayuwa?Kin yi aure da wani soja wanda kuka gina rayuwa da shi kuma kuka haifi ’ya’ya shida. wata rana, an tura shi yaki ba sake dawowa ba. Shekaru da yawa bayan haka, yayin da barazanar tayar da kayar baya ta fara bayyana a cikin garinku, ɗanku ya taka bam da ya fashe. Ba ku da tabbas ko zai tsira, kuka garzaya da shi asibiti a babban birnin tarayyar Najeriya, da fatan ba shi damar yin rayuwa. Bayan shekaru goma, har yanzu ba za ku iya komawa gida ba. Rikicin ya ci gaba da yaduwa. Yanzu, ana fitar da ku daga sansanin da kuke zama inda kuka zauna tsawon shekaru. Me zaku yi? Ina za ku je? Ke uwa ce mai yara takwas, kina rainon ‘ya’yanki a sansanin ‘yan gudun hijira dake babban birnin tarayyar Najeriya bayan tserewa mummunan harin da kungiyar ta’addancin Boko Haram ke kaiwa. Ta yaya zaki iya tinkarar barazanar rugujewar sansaninku, da kama danki, da kuma kwace baburan acabar da ki ka siya don samun abin rike rayuwa bayan duk kokarin ki na ganin kun samu rayuwa mai kyau na neman ya ci tura? Me za ku yi a lokacin da ’yan Boko Haram suka sace danku suka kuma koya mishi musu yaki, alhali kuna fuskantar kora a gidanku? Wannan jigon na #BIRBISHINRIKICI ta bibiyi rayuwar Ya Hauwa, wacce ta zama mace tilo da ke aiki a matsayin wakiliya a Borno, arewa maso gabashin Najeriya. Gudun Tsira Dauke Da Juna Biyu
Jummai mai dauke da cikin wata tara ta tsere daga garinsu da ke Nassarawa a Arewacin Najeriya bayan jin karar harbe-harbe! Wannan ba shine karo na farko da take tserewa tashin hankali ba. A cikin wannan shirin na #BIRBISHINRIKICI, mun ba da labarin asarar da sukayi da kuma gudun hijira.A cikin dare a cikin watan Disamba, 'yan ta'adda sun kai hari kan wata karamar al'umma a garin Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda suka bar gidaje a kone! Wannan shirin na #BirbishinRikici ya ba da labarin wata mata mai suna Tabitha mai shekaru 58, wadda ta rasu a daren. Sau Goma Sha Uku Tana Gudun Hijira
Sakamakon tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, an tilasta wa Binta Bukar mai shekaru 54 yin kaura sau 13. Wannan shirin na #BirbishinRikici ya ba da labarin gudun hijirar da ta yi, da asarar gida, da 'ya'yanta guda biyu.Shekaru Goma Sha Daya A Daure
Wannan shirin #BirbishinRikici ya ba da labarin Aisha, wacce kamar mijinta, sojojin Najeriya suka kama. Ta yi shekara 11 tana a tsare ba tare da jin ko ganin ’ya’yanta da al’umma ba. Yanzu ta sami 'yanci, tana gwagwarmayar sake shiga cikin al'umma. Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed Marubuciya: Sabiqah Bello Muryoyin Shiri: Sabiqah Bello Fassara: Rukayya Saeed Edita: Aliyu Dahiru Furodusa: Alamin Umar Babban Furodusa: Anthony Asemota Babban Mashiryi: HumAngle Media